Alexender Lavrinev ya bayyana hakan ne a taron manema labarai yammacin jiya birnin Asatana, bayan kammala zaman tattaunawar da ta gudana tsakanin Rasha, Iran, Turkiya da kuma gwamnatin Syria gami da tawagar masu tayar da kayar baya da ke dauke da makamai.
Bayanin bayan taron wanda ministan harkokin kasar Kazakhstan Girat Abdulrahmanov ya karanta, ya kunshi matakai wadanda za su kai ga gudanar da tattaunawa kai tsaye tsakanin gwamnatin Syria da kuma 'yan adawar siyasa gami da masu tayar da kayar baya da ke dauke da makamai, amma bayanin ya yi ishara da cewa tatataunawar ba ta hada da kungiyoyin ISIS da Nusra Front ba.
Tun daga cikin watan Maris na shekara ta 2011 ne kungiyoyin da ke dauke dauke da makamai suka fara kaddamar da hari a Syria da sunan yunkurin kifar da gwamnatin kasar, kamar yadda aka yi a kasar Libya, inda kasashen Qatar, Saudiyya da kuma Turkiya suka bayar da kudade da makamai ga kungiyoyin 'yan ta'adda daga ko'ina cikin duniya domin zuwa kasar Syria su kifar da gwamnatin kasar.288